Kofin Zakarun Nahiyoyi: Fifa za ta gwada sabon tsarin kididdiga kan 'yan wasa

'Yan wasan Jamus na atisaye Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan wasan Jamus ne zakarun duniya

A karon farko hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, za ta yi amfani da kananan kwamfutoci na hannu (tablet), wadanda ke kididdige bayanai a kan duk motsin da kowane dan wasa ya yi a wasan karshe da Jamus za ta yi da Chile na kofin zakarun nahiyoyi ranar Lahadin nan.

Masu fashin baki da kuma jami'an kula da lafiya na kowace kungiya su ma za su iya ganin duk wani abu da ya wakana, a lokacin wasan cikin dakika 30, da aukuwarsa.

Za a ba wa kowace kungiya kwamfutar guda uku, inda masu fashin bakinta su biyu kowanne zai samu daya, yayin da masu kula da lafiyar 'yan wasan za su samu daya.

Bayanan kowane dan wasa da za a rika watsawa ta kwamfutar sun hada da kididdigar yawan kwallon da ya bayar (passing), da yawan gudu da tarar kwallo da kuma yawan matsa abokan karawarsa da ya yi a wasan.

Hukumar kwallon kafar ta duniya za ta so samun bayani daga bangaren tawagar Jamus da ta Chile kan gwajin tsarin, wanda zai fara a kansu.