Gobarar Grenfell Tower : Hector Bellerin ya bayar da taimakon fan 19,050

Hector Bellerin a tawagar Spaniya ta 'yan kasa da shekara 21 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hector Bellerin ya kai wasan karshe na kofin kasashen Turai da tawagar Spaniya ta 'yan kasa da shekara 21

Dan wasan baya na Arsenal Hector Bellerin ya bayar da taimakon fan 19,050 ga wadanda gobarar dogon benen Grenfell Tower ta shafa.

Bellerin, mai shekara 22, ya yi alkawarin bayar da fan 50 na kowane minti da ya yi wa Spaniya wasa a gasar cin kofin kasashen Turai ta 'yan kasa da shekara 21 a Poland, kudin da za a mika su ga kungiyar agaji ta Red Cross ta Birtaniya.

Dan bayan ya yi wasan minti 381 a gasar da Spaniya ta kai wasan karshe ranar Juma'a, inda kuma ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Jamus.

Mutane akalla 80 suka mutu lokacin da gobara ta kama dogon benen na Grenfell Tower, da ke arewacin Kensington, a birnin Landan ranar 14 ga watan Yuni.

Shi ma dan wasan gefe na Manchester City da Ingila Raheem Sterling, wanda ya taso a yankin arewa maso yammacin Landan ya bayar da taimako mai yawa ga wadanda gobarar ta shafa.