Kasuwar 'yan wasa: Arsenal za ta yi barin kudi a kan Mbappe

Kylian Mbappe Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kylian Mbappe ya ci wa Monaco kwallo 23 a kakar nan

Arsenal na shirin yi wa Real Madrid shigar sauri a kan dan wasan Monaco na gaba Kylian Mbappe, mai shekara 18, inda za ta mika fan miliyan 125, kudin da ba ta taba kashewa ba a kan dan wasa, in ji jaridar Sunday Mirror.

Shi kuwa kociyan Bayern Munich Carlo Ancelotti hannunka mai sanda ya yi kan dan wasan gaba na Arsenal din Alexis Sanchez domin bude kofa ga dan wasan na Chile mai shekara 28, a bazara, yana mai bayyana dan wasan, wanda Manchester City ke so, amma kuma Arsenal ba ta son sayar wa abokan hamayyarta na Premier, da cewa gwarzo ne in ji London Evening Standard da Mail.

Kociyan Man City Pep Guardiola na shirin bar wa abokan hamayyarsu Man United golansu kuma na Ingila Joe Hart, mai shekara 30, kamar yadda Sunday Express ta ruwaito.

Yayin da kociyan the Reds din Jose Mourinho ke nuna cewa ko da ya samu Alvaro Morata, dan wasan da ya gaya wa abokansa cewa shi kam ya yanke shawarar tafiya Old Trafford, kuma ma har an kammala ciniki, zai so ya dauki dan gaban Everton Romelu Lukaku, shi ma mai shekara 24, in ji the Sun.

Shi kuwa kociyan Liverpool Jurgen Klopp zai iya yi wa Daniel Sturridge tarnaki ne don kada ya bar kungiyar saboda ba kananan kudi za a kashe ba wajen maye gurbin dan wasan na gaba mai shekara 27 in ji jaridar Sunday Mirror.

Dan wasan tsakiya na Arsenal Alex Oxlade-Chamberlain, mai shekara 23, ya yi watsi da tayin da Arsenal din ta yi masa na sabunta kwantiraginsa, kenan yana son tafiya a bazara idan wa'adin yarjejeniyarsu ya kare, inda zai tafi ba wata igiya a kansa a Janairun in ji Sunday Times.

Everton kuwa na shirin zawarcin Olivier Giroud ne daga Arsenal a kan fan miliyan 20, a kan dan wasan da West Ham da Marseille ta Faransa kowacce ke so in ji jaridar Sun.

Diego Costa na dab da nade tabarmarsa daga Chelsea wadda kociyanta ya ce masa ba ya bukatarsa domin komawa inda ya fito Atletico Madrid, amma kuma ko ya koma sai a watan Janairu yake da damar fara taka mata leda in ji Sunday Mail.

Dan bayan Roma kuwa Antonio Rudiger, mai shekara 24, ya shammaci abokansa ne da wani sako ta Instagram inda ya ce musu a lokacin bazara zai koma Chelsea in ji Metro.

Wakilin dan bayan Arsenal Hector Bellerin ya fara tattaunawa domin komawar dan wasan na Spaniya mai shekara 22 tsohuwar kungiyarsa Barcelona a bazaran nan in ji jaridar Metro.