Boksin: Wanda ya doke Pacquiao ya yi watsi da masu sukan alkalan damben

Jeff Horn (a dama) ya kai wa Manny Pacquiao naushi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jeff Horn (a dama) ya yi galaba a kan Manny Pacquiao wanda yawanci aka fifita zai yi nasara

Tsohon malamin makarantar da ya shammaci Manny Pacquiao ya kwace masa kambin duniya na ajin matsakaita nauyi na hukumar damben boksin ta WBO, ya yi watsi da maganar cewa bai cancanci nasarar ba.

Jeff Horn ya yi galaba a kan Pacquiao wanda dan majalisar dattawan kasarsa Philippines ne, sau tara yana zama zakaran duniya, bayan da hukuncin alkalan damben da aka yi a birnin Brisbane na Australia ranar Asabar, ya zo daya.

Masu horad da Pacquiao da wasu fitattun mutane da suka halarci damben, wanda aka yi a garin Jeff Horn, ciki har da tsohon zakaran duniya Lennox Lewis da gwanin dan kwallon kwando na Amurka Kobe Bryant sun soki hukuncin alkalan.

To amma shi Horn mai shekara 29, wanda kusan duniya ba ta san shi ba ya ce shi kam ya san ya cancanci nasarar.

A hirarsu da manema labarai ranar Litinin ya ce; ''Daman haka lamarin yake a ko da yaushe akwai wadanda za su ce sa'a kawai na yi ko kuma wani abu.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kociyan Manny Pacquiao, Freddie Roach ya ce akwai bukatar ya tattauna da dan danben a kan yin ritaya

''Ko da yaushe akwai 'yan-gaza-gani da za su ce ba ni ne ya kamata a ba wa nasara ba, amma ina ganin ni dai na yi nasara a damben. 'Yan Australiya da dama da sauran mutane a fadin duniya suna ganin ni na yi nasara.''

Kociyan Pacquiao Freddie Roach , ya ce zai tattauna da dan damben nasa a kan batun yin ritaya daga damben na boksin.

Sai dai Pacquiao, mai shekara 38 ya taya abokin karawar tasa murna kuma ya ce ya mutunta hukuncin alkalan.