John Terry ya yi watsi da 'yan Premier ya koma Aston Villa

John Terry da kofin Premier na karshe a Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption John Terry ya dauki kofinsa na Premier na biyar a kakarsa ta karshe a Chelsea

Tsohon kyaftin din Chelsea da Ingila John Terry ya yi watsi da tayin kungiyoyin Premier don ya martaba Chelsea, ya koma Aston Villa, tsawon shekara daya.

Dan wasan na baya mai shekara 36, wanda kwantiraginsa a Stamford Bridge ta kare ranar 30 ga watan Yuni ya koma kungiyar ta Chamionship ne saboda ba ya son ya je wata kungiya ta Premier wanda hakan zai sa ya kara a wasa da Chelsea.

Terry ya yi wa Ingila wasa sau 78, sannan ya taka wa Chelsea leda sau 717, kuma ya dauki kofin Premier na biyar a watan Mayu.

Villa ta gama a matsayi na 13 a gasar Championship a kakar da ta kare, amma kungiyar wadda Steve Bruce ke yi wa kociya na daga wadanda ake ganin za su samu tsallakawa zuwa Premier a kaka mai zuwa ta 2017-18.

A watan Yuni da ya kare kociyan Birmingham City Harry Redknapp, ya ce kungiyarsa ta yi zawarcin Terry, wanda a watan Afrilu ya sanar da cewa zai bar Chelsea.

Kungiyoyi biyu na Ingila kawai Terry ya taba yi wa wasa - Chelsea da Nottingham Forest, wadda ya yi zaman aro na dan takaitaccen lokaci a shekarar 2000.