Everton ta sayi Sandro Ramirez na Spaniya daga Malaga

Sandro Ramirez a hagu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sandro (a hagu) ya je Barcelona yana shekara 14 kafin ya bar Nou Camp a bara

Everton ta sayi dan wasan gaba na Spaniya Sandro Ramirez mai shekara 21 daga Malaga, kan yarjejeniyar shekara hudu, bayan da kungiyar ta cimma ka'idar sayar da shi ta fan miliyan 5.2 ta kwantriaginsa.

Sandro ya ci wa Malaga kwallo 14 a kakar da ta kare ta 2016-17, tun da ya koma can daga Barcelona a lokacin sayar da 'yan wasa na bara.

Bayan shi Everton na kuma fatan cinikin da take yi a kan dan wasan baya na Burnley kuma na Ingila Micheal Keane kan fan miliyan 25 zai tabbata.

Ana sa ran za a gudanar da gwajin lafiyar Keane mai shekara 24 a kungiyar kafin a kammala cinikin wanda nasa da na Sandro za su ci wa Everton fan miliyan 90.

Tuni kungiyar ta sayi mai tsaron ragar Sunderland na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 Jordan Pickford, a kan fan miliyan 30, sannan kuma ta dauko kyaftin din Ajax Davy Klaassen a kan kusan fan miliyan 24.

Haka kuma dan wasan gaba na Najeriya Henry Onyekuru daga kungiyar KAS Eupen a Belgium a kan fan miliyan bakwai, ko da yake zai yi zaman aro a Anderlecht na tsawon wata 12.