Kun san dan wasan da ya cancanci albashin dala miliyan 400?

Stephen Curry Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A bara Stephen Curry (a tsakiya) ya samu kyautar dan kwallon kwando mafi daraja a gasar NBA ta Amurka sau biyu a jere

LeBron James ya ce duk da cewa dan wasan kungiyar Golden State Warriors, Steph Curry zai kulla kwantiragi mafi kudi a tarihin kwallon kwando, kudin da za a rika biyansa bai kai yadda ya kamata a biya shi ba.

Curry mai shekara 29, wanda sau biyu ya samu lambar dan wasa mafi daraja a gasar kwallon kwando ta Amurka, NBA, yana shirin kulla kwantiragin da za a rika biyansa albashin dala miliyan 201 na shekara biyar, in ji wakilinsa.

Mujallar Forbes, ta ce hakan zai sa ya zama dan wasa na hudu da ya fi samun albashi a duk duniya.

LeBron James wanda ke yi wa kungiyar Cleveland Cavaliers wasa, wanda kuma shi ne dan wasan kwando da aka fi biya albashi, inda yake samun dala miliyan 33.2 a shekara ya ce kamata ya yi a biya Steph dala miliyan 400 a bazaran nan.

Kungiyoyin gasar kwallon kwando ta Amurka, NBA, suna da ka'idar iya albashin da za su biya 'yan wasansu, wanda a kaka mai zuwa zai kasance dala miliyan 99 a shekara, wanda daga ciki za su biya albashin dukkanin 'yan wasansu.

LeBron wanda ya dauki kofin gasar NBA uku yana sukar tsarin da ya sa za a kayyade kudin da za a biya dan wasa.