Tennis: Andy Murray ya fara kare kofin Wimbledon da nasara

Andy Murray Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Duk da nasarar Andy Murray ya nuna alamun ciwon kwibin da yake fama da shi

Gwanin tennis na daya a duniya Andy Murray na Birtaniya ya fara kare kofinsa na Wimbledon da nasara inda ya doke Alexander Bublik na Kazakhstan kai tsaye.

Dan wasan na yankin Scotland ya yi nasarar ne da ci 6-1 6-4 6-2 duk da ciwon kwibi da ya yi fama da shi kafin gasar, wanda sai a karshen mako ya bayyana cewa zai iya gasar.

Murray wanda shi ne na daya a duniya ya samu galaba a kan Bublik a cikin sa'a daya da minti 44.

A yanzu dan wasan mai shekara 30 zai fafata da dan Jamus Dustin Brown, wanda ya doke Rafael Nadal a 2015, a zagaye na biyu na gasar ta Wimbledon.

Image caption Irin kalubalen da Andy Murray zai fuskanta daga Dustin Brown

Murray yana son kafa tarihi irin na dan uwansa dan Birtaniya Fred Perry, wanda ya dauki kofin gasar sau uku a jere, kuma kofin zai sa ya zama na hudu na babbar gasa da ya dauka.

Haka kuma yana fuskantar kalubalen rike matsayinsa na daya a duniya, daga Nadal da Novak Djokovic da kuma Stan Wawrinka.