Venus Williams ta fashe da kuka kan hadarin motarta da ya kashe mutum

Venus Williams na kuka Hakkin mallakar hoto Wimbledon.Com
Image caption Venus Williams ta fashe da kuka lokacin taron manema labarai

Tsohuwar mai rike da kofin gasar tennis ta Wimbledon Venus Williams ta fashe da kuka lokacin da 'yan jarida suka yi mata tambaya a kan hadarin motar da ta yi wanda ya yi sanadin mutuwar wani mutum a Florida.

Venus Williams, mai shekara 37, za ta iya fuskantar shari'ar kisan kai daga iyalan mutumin bayan da 'yan sanda suka zarge ta da laifi a hadarin.

Ba'amurkiyar ta halarci taron manema labarai ne bayan da ta doke Elise Mertens a zagayen farko na gasar ta Wimbledon a ranar Litinin din nan.

A game da hadarin Williams ta ce : "Ba za ta iya bayyana irin kuncin al'amarin ba. Ta ce gaba daya ta kasa magana.

Daga nan ne sai ta fara hawaye tana kuma, har ta kai sai da ta bar dakin taron manema labaran, ta je ta natsu kafin ta dawo ta amsa 'yan tambayoyi a kan wasan da ta yi.

Hadarin wanda ya faru a ranar tara ga watan Yuni ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum mai shekara 78, mai suna Jerome Barson.

Venus Williams, wadda sau biyar ta dauki kofin Wimbledon, ta doke Mertens mai shekara 21, wadda a karon farko take wasa a gasar da ci 7-6 (9-7) 6-4.

Cikin sauki daman ta taba doke Mertens din a zagayen farko na gasar Roland Garros da ci 6-3 6-1.

Yanzu Williams za ta kara a zagaye na biyu na gasar da Wang Qiang ta China, wadda ta doke Chang Kai-chen ta Taiwan da ci 6-3 6-4.