John Terry na burin zama kociyan Chelsea

John Terry da rigar Aston Villa
Image caption Burin Villa shi ne shiga Premier in ji John Terry

John Terry ya ce zai yi matukar farin ciki idan ya zama kociyan tsohuwar kungiyarsa Chelsea bayan ya yi ritaya daga wasa.

Dan wasa na baya mai shekara 36, ya koma kungiyar Aston Villa wadda take gasar kasa da Premier ta Championship, na tsawon shekara daya ranar Litinin, bayan da ya bar zakarun na Premier a karshen watan Yuni.

Jaridu da dama sun ruwaito Terry yana cewa, a kullum shi yana son ya zama gwani-na-gwanaye, kuma idan hakan zai kasance a aikin kociya ne, to a Chelsea yake son ya zama.

Sai dai tsohon kyaftin din na Ingila, wanda ya buga wa kungiyar wasa 717 kuma ya dauki kofin Premier biyar da ita, ya ce abu ne mai wuya ka fara aikin kociya da kungiya kamar Chelsea.

A lokacin da ake gabatar da shi ga magoya baya lokacin da ya koma Aston Villa Terry ya ce, matsalar da zai fuskanta wajen karawa da Chelsea, na daya daga dalilan da ya ki amsa tayin kungiyoyin Premier.

Ko da yake Terry ba zai yi kociya ba ne a Villa, amma dai zai koyi abubuwa daga kociyanta Steve Bruce da kuma darektanta na wasa Steve Round, wanda Terry ya yi aiki da shi a lokacin da yake taka wa Ingila leda.