Tennis: Kullum sai na yi wanka da ruwa mai sanyi kamar kankara - Murray

Andy Murray Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Iyalina su ne mafi muhimmanci a rayuwata, kuma aure da haihuwa da na yi sun taimaka wa wasana - Andy Murray

Gwanin tennis na daya a duniya kuma mai rike da kofin Wimbledon, Andy Murray na Birtaniya, ya ce kullum da daddare sai ya yi wanka da ruwa mai sanyi kamar kankara domin shirya wa gasar ta bana.

Murray dan yankin Scotland ya ce ya yi sa'a domin daman ya saba wanka da ruwa mai tsananin sanyi, domin kawai ya tunkari gasar da kyau.

Mai rike da kofin na Wimbledon ya ce ya dan sauya wasu abubuwan da yake yi na yau da kullum tun lokacin da kugunsa ya fara ciwo a makon da ya wuce, amma yanzu dabarar da ya yi ta taimaka masa.

Dan tennis din ya ce kusan ya kara yin wasu abubuwan na minti 20, inda yake wankan ruwan sanyin na tsawon minti takwas zuwa goma, da kuma motsa jiki shi ma na tsawon minti takwas zuwa goma.

Hakan na nufin yana wankan ruwan sanyin karara sau biyu, daya a filin wasan na Wimbledon daya kuma a gida kafin ya kwanta.

Ba kowa ba ne zai iya bin wannan tsarin idan yana son samun kyakkyawan barci, in ji Murray, wanda ya ce shi kam ya yi sa'a domin tsawon shekaru ya saba da wanka da ruwan sanyin karara, ''kuma bai dame ni ba, garau nake ji.''

Murray ya ce daman tun da dadewa yana fama da ciwon kugu, ya warke ya dawo, tun yana shekara 22 ko 23, saboda haka ba sabon abu ba ne a wurinsa, amma cikin 'yan kwanaki bayan ya yi wasa da Stan Wawrinka a gasar Faransa sai ciwon ya yi tsanani.