Tennis: Federer da Djokovic sun kai zagaye na biyu a Wimbledon

Federer da Dolgopolov Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Minti 43 kawai Federer da Dolgopolov suka yi a fili

Tsoffin zakarun Wimbledon Roger Federer da Novak Djokovic sun kai zagaye na biyu na gasar ta bana ba tare da an tashi daga wasansu ba bayan da abokan karawarsu suka hakura saboda rauni.

Gwani na uku a wasan na tennis Federer yana gaban abokin karawarsa Alexandr Dolgopolov da ci 6-3 3-0, lokacin da dan Ukrain din ya dakata da wasan saboda ciwon idon sawu bayan minti 43.

Haka shi ma gwani na biyu na duniya Djokovic ya kai wasan zagaye na gaba bayan da abokin fafatawarsa Martin Klizan ya bar wasan saboda ciwon sharaba ana gabansa da ci 6-2 2-0 a minti na 40.

Djokovic dan Serbia ya ce: "Ba za ka taba kaunar kammala wasa ta haka ba."

Ya ce ya ji cewa Klizan yana da matsala tun kafin ya shigo fili. ''Gaskiya za ka ga yadda ba ma ya iya bin kwallo idan ta yi masa nisa, sai kawai ya kyale ta.''

Djokovic mai shekara 30, a yanzu zai fafata da Adam Pavlasek dan kasar Czech a zagaye na biyu ranar Alhamis yayin da yake neman daukar kofin Wimbledon dinsa na uku.

Shi kuwa Federer wanda sau bakwai yana daukar kofin a yanzu kenan ya kama hanyar cin na takwas a gasar da ake yi a Landan.

Federer dan Switzerland yanzu ya yi nasara a wasa 85 kenan na Wimbledon, inda ya zama namijin da ya fi kowa cin wasa a gasar - Jimmy Connors ya ci sau 84, sai Boris Becker mai nasara 71 da kuma Pete Sampras wanda ya ci wasa 63 a gasar.

Dan Canada Milos Raonic gwani na shida, wanda ya zo na biyu a gasar a bara ya fitar da Jan-Lennard Struff na Jamus da ci 7-5 (7-5) 6-2 7-6 (7-4), a wasansa na farko.