Palace ta yi maganin kwarin ciyawa da tafarnuwa a filinta

Filin Crystal Palace, Selhurst Park Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mai kula da filin ya ce ruwan tafarnuwa yana da wari sosai amma ya fi maganin kwarin

Crystal Palace ta yi amfani da ruwan tafarnuwa domin maganin wasu kananan kwari da ido ba ya iya gani, wadanda ke yi wa ciyawar filinsu illa.

Kungiyar ta yi amfani da wannan dabara ne domin shirya filin domin tunkarar gasar Premier da ke tafe.

Daman filin na Selhurst Park yana fama da matsalar kwarin wadanda suke illa ga saiwar ciyawar, su sa ta yi saurin lalacewa.

Babban jami'in da ke kula da filin Bruce Elliott ya ce ruwan tafarnuwa yana da wari sosai amma kuma shi ne ke maganin kwarin sosai.

A ranar biyar ga watan Agusta Palace za ta yi wasanta na sada zumunta na farko na shirin tunkarar kaka da kungiyar Schalke ta Jamus.

Palace wadda Frank de Boer ke yi wa kociya za ta karbi bakuncin Huddersfield a ranar farko ta gasar Premier mai zuwa, 12 ga watan Agusta.