Jamus: Ginter ya bar Dortmund saboda matsi

Matthias Ginter Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matthias Ginter ya yi wa Jamus wasa 14

Borussia Monchengladbach ta sayi dan wasan baya na Jamus Matthias Ginter daga Borussia Dortmund a kan euro miliyan 17, bayan da ya bukaci tafiya saboda matsin neman wuri da sauran 'yan wasa.

Dan wasan na tawagar Jamus mai shekara 23 ya kulla kwantiragin zama a can har zuwa shekara ta 2021.

Ginter na cikin tawagar Jamus da ta doke Chile 1-0 a wasan karshe na kocin zakarun nahiyoyi ranar Lahadi.

Darektan wasa na Dortmund Michael Zorc ya ce Ginter ya bayyana bukatarsa ta tafiya ne saboda gogayyar da ake yi ta neman wuri tsakanin 'yan wasa a kungiyar.