Lille ta sallami 'yan wasa 11 har da Vincent Enyeama na Najeriya

Vincent Enyeama Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Enyeama, wanda ya koma Lille a watan Yuni na 2011, ya yi mata wasa 164

Tsohon mai tsaron ragar tawagar Najeriya Vincent Enyeama na daya daga cikin 'yan wasa 11 da sabon kociyan kungiyar Lille ta Faransa, Marcelo Bielsa ya ce ba ya bukatarsu.

Sabon kociyan na kungiyar ta Faransa, dan Argentina ya kuma gaya wa dan wasan Zambia Stoppila Sunzu da dan Tunisia Naim Sliti da kuma dan Ivory Coast Junior Tallo cewa su ma ba sa cikin tsarinsa.

A kakar da ta kare ne Enyeama wanda ya yi wa Najeriya wasa sau 101, ya sabunta kwantiraginsa, kuma zai iya zabar ya bi sahun Tallo na Ivory Coast wanda ya ce shi kam yana da kwantiragi na sauran shekara biyu da kungiyar kuma zai mutunta yarjejeniyar.

Ya ce ta hanyar sakon kar-ta-kwana na waya aka gaya masa, tun da kungiyar ce take son su tafi za su jira su gani nan da karshen kasuwar saye da sayar da 'yan wasa yadda lamarin zai kasance, ba ya cikin sauri.

Tuni kungiyar ta sayi wasu 'yan wasa da suka hada da mai tsaron ragar tawagar Burkina Faso Herve Koffi sakamakon rashin kokarin da lIlle din ta yi inda ta gama kakar da ta wuce a matsayi na 11