Alexandre Lacazette zai koma Arsenal kan 45m

Alexandre Lacazette

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alexandre Lacazette ya fara bugawa tawagar kwallon kafar Faransa ne a shekarar 2013

Dan wasan Lyon Alexandre Lacazette zai kammala yarjejeniyar fam miliyan 45 na komawa Arsenal ranar Laraba bayan ya kammala gwaje-gwajen lafiya.

A da dai an ki tayin da Gunners suka yi wa dan asalin Faransan mai shekara 26, amman tattaunawa ta ci gaba.

Jumullar kudinsa idan aka hada da wasu alawus-alawus zai kai fam miliyan 52, abin da zai fi fam miliyan 42.4 da Arsenal ta biya wa Mesut Ozil lokacin da ya bar Real Madrid a shekarar 2013.

Lacazett, wanda ya buga wasanni 11 wa Faransa, shi ne dan wasa na biyu cikin wadanda suka fi shan kwallo a gasar Ligue 1 a kakar bara inda ya sha kwallaye 28.

Ana kyautata zaton cewar komawarsa arewacin Londan zai kammalu ranar Laraba saboda sanarwar yarjejeniyar ta yi dai dai da kasuwar hannayen jarin Farsansa inda ake sayar da hannayen jarin kungiyar.

Lacazette ya sha kwallaye 129 a wasanni 275 a dukkan gasar da ya buga wa Lyon tun da ya fara taka leda a kungiyar a kakar 2009-10.

A kakar bara dan wasan Paris St-Germain, Edinson Cavani, da ya sha kwallaye 35 shi ne kadai ya fi shi shan kwallaye a gasar Ligue 1 din.