Manchester United ta amince ta sayi Romelu Lukaku kan fan miliyan 75

Romelu Lukaku Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Romelu Lukaku ya shafe shekara hudu a Everton, inda ya zira kwallo 81

Manchester United ta amince ta sayi dan wasan gaba na Everton Romelu Lukaku kan kudi fan miliyan 75.

Dan kwallon mai shekara 24 na kasar Belgium ya zira kwallo 25 a gasar Firimiyar da aka kammala.

United, wacce ta dade tana neman Lukaku, ba za ta ci gaba da neman dan wasan Real Madrid Albaro Morata ba.

Kuma BBC ta fahimci cewa daukar Lukaku ba shi da alaka da batun da ake yi na komawar Wayne Rooney zuwa Everton.

Tawagar ta Jose Mourinho na fatan kammala cinikin dan wasan kafin kungiyar ta tafi Amurka domin atisayi ranar Lahadi.

Lukaku na cikin jerin sunayen 'yan wasa da Mouribho ya bai wa mataimakin shugaban kungiyar, Ed Woodward kafin karshen kakar wasan bara.

A da ana ganin Lukaku zai koma tsohuwar kungiyarsa ta Chelsea ne, wacce ya je daga Anderlecht a 2011.

Mourinho ne ya sayar da dan wasan gaban a kan fam miliyan 28 ga Everton a lokacin yana kocin Chelsea a karo na biyu a shekarar 2014.

Mino Raiola shi ne wakilin Lukaku, kuma shi ne wakilin Paul Pogba, da Zlatan Ibrahimovic da Henrikh Mkhitaryan - 'yan wasa uku da United ta saya a kakar wasan bara.

Labarai masu alaka