Real Madrid za ta yi wasa uku a Yuli

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ce ta lashe kofin Zakarun Turai kuma na 12 jumulla

Kungiyar Real Madrid za ta buga wasa uku a cikin watan Yulin shekarar nan kafin a fara kakar wasanni ta 2017/18.

Madrid wadda ta lashe kofin La Liga da aka kammala ta shiga gasar International Champions Cup da za a yi a Amurka, kuma karo na hudu a jere kenan da kungiyar za ta fafata a wasannin.

Real za ta fara karawa da Manchester United a ranar 23 ga watan Yulin a filin wasa na Santa Clara da ke California.

Wasa na biyu kuwa za ta fafata ne da Manchester City a ranar 27 ga watan a filin wasa na Memorial Coliseum da ke Los Angeles.

Madrid za ta buga wasa na uku a watan na Yuli da Barcelona ranar 30 ga wata a wasan El Classico a filin wasa na Hard Rock da ke Miami.