Real Madrid ta dauki Theo Hernandez

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Theo Hernandez mai shekara 19 mai tsaron baya ya amince ya buga wa Real Madrid wasa zuwa shekara shida

Real Madrid ta sanar da daukar dan kwallon Atletico Madrid, Theo Hernandez kan yarjejeniyar shekara shida.

Madrid wadda ta sanar da daukar dan kwallon mai tsaron baya mai shekara 19 a shafinta na intanet a ranar Laraba, ba ta fayyace kudin da ta dauki dan wasan ba.

Sai dai kuma kungiyar ta ce za ta gabatar da shi a gaban magoya bayanta a Santiago Bernabeu a ranar Litinin sannan ya gana da 'yan jarida.

Real Madrid ce ta lashe kofin La Liga na Spaniya da aka yi a 2016/17, yayin da Atletico Madrid ta yi ta uku a gasar.

Labarai masu alaka