Barcelona za ta kece raini da Juventus

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ce ta yi ta biyu a gasar La Liga ta 2016/17

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona za ta yi wasa hudu a nan gaba kafin a fara gasar wasannin kakar da za a shiga a cikin watan Agusta.

Barcelona za ta fara karawa da Juventus a Amurka a gasar International Champions Cup a ranar 23 ga watan Yuli.

Juvuntus ce ta fitar da Barcelona a gasar Zakarun Turai da aka kammala, wadda Real Madrid ta lashe kofin kuma na 12 jumulla.

A kuma ranar 27 ga watan za ta kece raini da Manchester United, sannan ta fafata da Real Madrid a ranar 30 ga watan a dai gasar da za a yi a Amurka.

Barcelona za ta buga wasa na gaba a ranar 7 ga watan Agusta da Chapecoense a filinta na Camp Nou.