Arsenal ta kammala daukar Lacazette

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alexandre Lacazette ya ci kwallo 100 a wasa 203 da ya yi wa Lyon da kuma 11 da ya ci wa Faransa

Arsenal ta kammala sayen Alexandre Lacazette daga Lyon kan kudi fan miliyan 46.5 kan yarjejeniyar shekara biyar.

Kudin da aka sayi dan kwallon ya kai fam miliyan 52.6 idan aka hada da wasu tsarabe-tsarabe, wanda hakan ya dara yadda Arsenal ta dauko Mesut Ozil na kudi fam miliyan 42.4 daga Real Madrid a 2013.

Ana sa ran Lacazette mai shekara 26 zai ziyarci Sydney tare da 'yan wasan Arsenal domin buga wasan sada zumunta da za ta yi a mako mai zuwa.

Lacazette wanda ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Faransa wasa 11 shi ne na biyu a yawan cin kwallo a gasar Faransa, inda ya ci 28, a kakar da ta kare.

Dan wasan ya ci kwallo 129 a wasa 275 da ya buga wa Lyon tun daga lokacin da ya fara buga mata tamaula a 2009/10.

Labarai masu alaka