Kun san kulob din da ya fi fice a Turai?

European Season Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu wasannin da aka lashe kofi a gasar kasashen Turai a kakar 2016/17

A cikin watan gobe ne za a fara gasar wasannin kwallon kafar kungiyoyin kasashen nahiyar Turai ta kakar shekarar 2017/18, ga yadda aka kammala wadda ta kare.

A ranar 29 ga watan Mayu aka kammala gasar cin kofin Premier na Ingila ta 2016/17 wanda kulob din Chelsea ya lashe wato kofinsu na shida jumulla.

Kungiyar Leicester City ce ta lashe kofin Premier a wani abu na ba sababba, inda ta buga wasa 38 ta hada maki 81, kuma kofin farko da ta ci tun bayan kafa kungiyar sama da shekara 132.

Sai dai a bana Leicester ta kare ta 12 a kan teburi da maki 44.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea ce ta ci kofin Premier na 2016/17 kuma na shida jumulla

Wasannin karshe a gasar da aka kammala an yi tata burza wajen neman matakin hudun farko, matsayin da za a fitar da wadanda za su wakilci Ingila a gasar cin kofin zakarun Turai ta badi.

Kodayake Chelsea da Tottenham su ne keda gurbin na daya da na biyu, daga karshe Manchester City ta yi ta uku Liverpool ta hudu bayan da ta doke da ci Middlesbrough 3-0.

Arsenal wadda ta doke Everton 3-1 ta biyar ta yi, kuma a karon farko za ta buga gasar zakarun Turai ta Europa, bayan shekara 20 a jere tana buga gasar Zakarun Turai.

Sai dai kuma Arsenal ta ci kofin FA bayan da ta doke Chelsea a Wembley da ci 2-1.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal za ta buga Europa a kakar 2017/18

Sannan Arsenal ta sake tsawaita yarjejeniyarta da Arsene Wenger domin ya ci gaba da jan ragamar kungiyar zuwa shekara biyu, duk da wasu magoya bayan ba su so hakan ba..

Manchester United wadda ta sayi Paul Pogba daga Juventus kan kudi sama da fam miliyan 89 a matsayin wanda yafi tsada a duniya ta dauko Henrik Miiktahriyan da Victor Lindolof da Zlatan Ibrahhimovic, jumulla ta kashe sama da fan miliyan 146 a mataki na shida ta kare a Premier bara.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pogba shi ne dan wasan da ya fi tsada a kakar 2016/17

Sai dai kuma United ta taka rawar gani a gasar cin kofin zakarun Turai ta Europa inda ta lashe shi bayan da ta doke Ajax 2-0 a wasan karshe, hakan na nufin za ta buga gasar Zakarun Turai na 2017/2018.

A dai ranar karshe da za a rufe wasannin Premier Walter Mazzarri ya jagoranci Watford, bayan da tuni aka kore shi daga kungiyar, shi kuwa kocin Southampton Claude Puel ya sha ihu a wajen magoya baya duk da kulob din ya kammala a mataki na takwas, matsayin da ake ganin ya taka rawar gani.

Tun kafin fara Premier bara, an yi hasashen cewa gasar za a fafata ne tsakanin Pep Guardiola na Manchester City da Jose Mourinho na Manchester United.

Ashe ba a nan take ba, inda Antonio Conte mai horar da Chelsea ya nuna cewa shi ba kanwar lasa ba ne ya kuma dagula lissafin masana tamaula.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Conte ne ya jagoranci Chelsea ta ci kofin Premier a kakar farko

Duk da doke Sunderland 5-1 da Chelsea ta yi a ranar da aka rufe Premier da yin bankwana da John Terry, kungiyar ta kafa tarihin cin wasa 30 daga 38 da ta fafata a kakar 2016/17.

Kungiyar ta ci kofin ne da zarar maki bakwai tsakaninta da ta biyu.

Tuni Hull City da Midlesbrough da Sunderland suka yi ban kwana da Premier, inda Newcastle da Brighton and Hove Albion, da Huddesfield suka maye gurbinsu a wasannin da za a yi a bana.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ce ta lashe kofin zakarun nahiyoyin duniya

A Spain an yi gumurzu an kai ruwa rana, domin sai a wasan karshe ne Real Madrid ta ci kofin La Liga, bayan tafiyar kan-kan-kan da ta dinga yi da Barcelona.

Ita kuwa Barcelona wadda ta yi ta biyu a La Liga ta dauki Copa del Rey kacal duk da cewa ta amincewa kocinta Luis Enrique ya gwada sa'arsa a wata kungiyar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ce ta dauki Copa del Rey na Spaniya

Madrid ta lashe kofin La Liga bayan zaman jiran shekara biyar na biyu a cikin shekara takwas.

A Cardiff ne, Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai bayan da ta doke Juventus 4-1 ta zama ta farko da ta ci kofin guda biyu a jere tun bayan da aka sauya masa fasali kuma na 12 a tarihi.

Madrid sai da ta yi jiran shekara 59 rabon da ta dauki kofin zakarun Turai da na gasar Spaniya a lokaci guda.

Real din ta yi wannan bajintar duk da hanata sayen 'yan wasa da hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta yi, bayan da aka same ta da laifin karya ka'idar daukar matasan 'yan kwallo tare da Atletico Maadrid.

Madrid ta taka rawa matuka tun bayan da ta dauki Zinadine Zidane a matsayin kociyanta a Janairun 2016, bayan da ya maye gurbin Rafa Benitez.

Kocin bai yi kasa a gwiwa ba, inda ya lashe kofin zakarun Turai biyu da European Super Cup da kofin zakarun nahiyoyin duniya da na La Liga, kuma sai da ya yi wasa 40 a jere ba tare da an doke Madrid ba.

Kuma Real sai da ta zura kwallo a ragar kowacce kungiyar da ta fafata da ita a wasannin na La Liga.

Barcelona ta matsa kaimi matuka inda Messi da Neymar da Suarez suka ci kwallo 116 a tsakaninsu, ciki har da cin Real Madrid, Atlétic Bilbao, Athletico Madrid, Valencia and Sevilla, ya yin da Alavés, Celta Vigo, Deportivo da kuma Málaga suka taka mata burki.

Sevilla da Atletico sun taka rawar gani a gasar ta La Liga amma daga karshe suka kasa kai bantensu.

Wadanda suka yi ban kwana da La Liga da aka yi sun hada da Sporting Lisbon da Osasuna da Granada, ya yin da Levente Girona da kuma Getafe suka maye gurbinsu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Munich ce ta lashe kofin Bundesliga

A Jamus Bayern Munich ce ta yi nasarar cin Bundesliga na biyar a jere kuma na 26 a tarihi bayan da aka kammala wasannin 2016/17.

Munich ta dauko Carlo Ancelotti wanda ya maye gurbin Pep Guardiola.

Munich ta fara kakar bara da kafar dama inda ta doke Borussia Dortmund a wasan Super Cup na Jamus.

A wasan mako na 11 ne Bayern ta bar mataki na daya a kan teburi wanda ta rike sama da shekara daya, bayan da Dortmund ta doke ta da ci daya mai ban haushi.

Wasa na gaba ta yi kunnen doki 1-1 da Hoffenheim, sai kungiya mai tashe RB Leipzig ta haye mataki na daya a kan teburin., amma ba a dauki lokaci mai tsawo ba Munich ta karbi gurbinta.

Haka dai ta dinga gurgurawa har ta ci Bundesliga, Rb Leipzig ta yi ta biyu Dortmund ce ta uku, su ne kungiyoyin da za su buga gasar Zakarun Turai ta badi kai-tsaye.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Juventus ce ta lashe Serie A na Italiya kuma na shida a jere

A gasar Serie A ta Italiya Juventus ce ta kafa tarihin lashe Scudetto sau shida a jere.

Yakin neman mataki na biyu kuwa Roma ta kwata a hannun Napoli a wasan karshe a kakar da aka kammala.

Kungiyar Atalanta ce ta bayar da mamaki a wasannin da aka yi inda ta karbi matsayin na hudu ta bar Lazio da cizon yatsa.

Tun fara gasar kungiyar Pescara ba ta tabuka rawar gani ba, ita kuwa Palermo ta yi wa kanta sakiyar da ba ruwa bayan da ta rinka sauya masu horar da ita, hakan kuma bai hana ta ficewa daga wasannin Serie A ba.

Ita kuwa Crotone wadda aka yi yakinin za ta ci kasa a gumurzun da aka kammala sai a wasan karshe ta yunkura wanda hakan ya sa ta rikito da Empoli daga gasar ta Serie A.

Labarai masu alaka