Leicester City ta dauki Vicente Iborra

Leicester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Iborra ya koma Sevilla da taka-leda daga Levante

Leicester City ta dauki dan wasan Sevilla, Vicente Iborra kan kudin da ake cewa zai kai fam miliyan 10.5.

Dan wasan mai shekara 29 mai wasan tsakiya wanda ya dauki Europa Cup a Sevilla, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara hudu.

Iborra ya buga wa Sevilla wasa 172 ya ci kwallo 30 tun komawarsa can da murza-leda daga Levante a 2013.

Jaridun Spaniya ne ke wallafa cewar kudin da Leicester City ta biya kan dan kwallon ya kai fam miliyan 10.5.