Sadio Mane na daf da dawowa atisaye

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sadio Mane ya koma iverpool kan yarjejeniyar shekara biyar a Yunin 2016

Dan wasan Liverpool Sadio Mane na daf da dawowa fagen atisaye nan da kwana 10, bayan da ya yi jinyar rauni a gwiwar kafarsa.

Mane bai buga sauran wasannin Liverpool takwas da aka kammala Premier ba, sakamakon raunin da ya yi a karawa da Everton a ranar 1 ga watan Afirilu.

Sai dai kuma dan kwallon na tawagar Senegal ba zai buga wa Liverpool wasannin gwaji da za ta yi domin tunkarar gasar bana ba.

Mane ya ci wa Liverpool kwallo 13 a wasa 27 da ya buga a gasar Premier da aka kammala tun komawarsa can da taka-leda daga Southampton kan kudi fam miliyan 34 a watan Yuni.

Liverpool za ta fara yin gasar Premier ta bana a ranar 12 ga watan Agusta, inda za ta karbi bakuncin Watford a Anfield.