Nigeria ce ta shida a iya kwallo a Afirka

Fifa Rankin Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nigeria ta yi kasa zuwa matsayi na shida a jerin Fifa da ta fitar a ranar Alhamis

Tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Nigeria ta yi kasa zuwa mataki na shida a jerin kasashen da suke kan gaba a iya taka-leda a Afirka.

A jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta fitar a ranar Alhamis ya nuna Nigeria ce ta 39 a jerin wadan da suke kan gaba a murza-leda a duniya.

Kasar Masar ce ta daya a Afirka, sai Senegal ta biyu Jamhuriyar Congo ta uku sannan Tunisia ta hudu da Kamaru a mataki na biyar.

A ranar 1 ga watan Yuni hukumar kwallon kafa ta duniya ta fitar da sakamakon watan, inda Nigeria ce ta hudu a Afirka kuma ta 34 a duniya.

Jamus ita ce ta daya a iya kwallo a duniya, matakin da ta rasa shekara biyu, bayan da ta maye gurbin Brazil wadda ta dawo matsayi na biyu.

Argentina ce ta uku sai Portugal wadda ke rike da kofin nahiyar Turai a mataki na hudu.

Labarai masu alaka