Iheanacho ya kusa komawa Leicester kan kudi £25m

Kelechi Iheanacho Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kelechi Iheanacho ya sha kwallaye 21 a wasanni 64 da ya buga wa Manchester City

Dan wasan gaba na Manchester City, Kelechi Iheanacho, yana gab da kammala yarjejeniyar fam miliyan 25 ta komawa Leicester City da taka leda.

Tattaunawar dan Najeriyar mai shekara 20 da Foxes ta yi nisa, kuma yana shaukin sauya sheka zuwa Leicester City.

Iheanacho ya sha kwallaye 21 cikin wasanni 64 da ya buga wa Manchester City tun da ya koma kulob din da taka leda a shekarar 2015.

A watan Augustan bara ne dai ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da za ta tsawaita zamansa a kublob din, amman isowar dan wasan Brazil, Gabriel Jesus ta takaita iya lokacin wasan da yake samu a kungiyar.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba