Wanne hali Lukaku da Conte da Rooney ke ciki?

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

Inter Milan tana son ta sayi Alexis Sanchez, mai shekara 28, na Arsenal (Gazzetta dello Sport, via Daily Mirror)

Stoke City na fuskantar jinkiri kan yunkurinsu na sayan Fabian Delph, mai shekara 27, a daidai lokacin da dan wasan tsakiyan ke bukatar warware wasu batutuwa kan yarjejeniyarsa a Manchester City kafin su sallame shi. (Stoke Sentinel)

QPR ta yarda ta sayar da dan shekara Josh Bowler dan shekara 18 ga Everton a wata yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 4. (London Evening Standard)

Kungiyar Everton tana son ta dawo da Wolfsburg mai shekara 19 Anton Donkor a matsayin dan wasan aro bayan an takaita lokacin da zai ci gaba da zama a Goodison Park a kakar bara. (Liverpool Echo)

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Robert Snodgrass ya koma West Ham daga Hull City a watan Janairu

Kungiyar Sunderalad da ke wasa a gasar zakarun turaitana fatan kawo dan wasan West Ham, Robert Snodgrass, mai shekara 29, filin wasanta da ake kira the Stadium of Light. (Newcastle Chronicle)

Watford za ta iya yunkurin sayo dan wasan Napoli, Ivan Strinic mai shekara 29 da kuma dan wasan Sassuolo, Gregoire Defrel. (Sky Italia, via Hertfordshire Mercury)

An bai wa Manchester City kudin da ya kai fam miliyan 1.75 domin sayan dan shekara 17 Tyrese Campbell. Dan tsohon dan wasan Arsenal da Everton Kevin Campbell ya bar kungiyar czuwa Stoke City a lokacin zafin da ya wuce. (Manchester Evening News)

Middlesbrough na son sayan dan wasan Derby County mai shekara 24, Cyrus Christie. (Derby Telegraph)

Ana tababa kan makomar kociya Antonio Conte a Chelsea domin dan asalin Italiyan ya ji haushin gazawar da kungiyar ta yi kasuwar 'yan wasan ta lokacin zafi. (Daily Mirror)

Yunkurin Manchester United na sayan Romelu Lukaku ba shi da alaka da wata yarjejeniyar da za ta kai kaftin din United Wayne Rooney, mai shekara 31, zuwa Goodison Park. (Liverpool Echo)

Duk da haka, ana tsammanin Chelsea za ta matsa kaimi wajen nuna son sayan Lukaku,mai shekara 24, duk da cewar United ta cimma yarjejeniya kan kudifam miliyan 75 da Everton domin cinikin dan wasan. (Guardian)

Dan wasan gaban Real Madrid, Alvaro Morata, mai shekara 24, ya shiga tsaka mai wuya bayan cinikin Lukaku da United ta yi, bayan an gamsar da shi cewar zai bar Spaniya zuwa Old Trafford.(Independent)

Dan asalin Belgium, Lukaku ya yarda da yarjejeniya mai tsawo da ya kai fam 250,000 a ko wane mako da kungiyar Jose Mourinho. (Daily Star)

Chelsea za ta iya fuskantar matsalar dan wasan gaban lokacin Diego Costa, mai shekara 28, ya fara adabo ga abokan wasansa bayan an gaya masa baya cikin shirin Conte na kakar bara .(Daily Telegraph)

A yanzu kuma zakarun gasar Firimiya sun mayar da hanakalinsu kan dan wasan gaban Swansea Fernando Llorente, mai shekara 32, bayan sun gaza samun dan asalin Spain a bashia watan Janairu. (Evening Standard)

Barcelona ta fusata da tsohon kaftin dinta Carles Puyol, bayan dan wasan da yake wakilta - Eric Garcia - ya yanke hukuncin ficewa daga kungiyar zuwa Manchester City. (Independent)

Arsenal na son sayan dan wasan Eintracht Frankfurt, Aymen Barkok. (Spox - via Daily Express)

Kungiyar Marseille ta Faransa na sahun gaba cikin masu son sayan dan wasan Arsenal Olivier Giroud, mai shekara 30,a wata yerjejeniya ta fam 24.7m bayan Gunners ta kammala sayan Alexandre Lacazette. (Daily Telegraph)

Gunners sun ki su ba da abun da Leicester City ke nema kan Riyad Mahrez, amman ana sa ran dan shekara 26 zai bar Foxes a lokacin bazara.(Daily Star)

An sanar da tsohon dan wasan Newcastle United Hatem Ben Arfa, mai shekara 30, cewar zai iya barin Paris St-Germain. (L'Equipe - via Newcastle Chronicle)

Demarai Gray, mai shekara 21, yana son tabbaci daga Leicester game da samun gurbin shiga tawaga ta farko a lokacin da ake kara samun masu son sayan dan wasan na Ingila kamar Liverpool da Tottenham. (Daily Mirror)

Guangzhou Evergrand ta ki ta sayar da tsohon dan wasan Spurs Paulinho, mai shekara 28, ga Barcelona duk da cewar kungiyar ta yi wa kulob din tayin fam miliyan 22 . (Sky Sports)

Stoke tana tattaunawa da domin samun dan wasan Manchester CityFabien Delph, mai shekara 27, kan bashi. (Stoke Sentinel)

Real Madrid ta yi tattaunawar sirri da dan wasan tsakiyar PSG Marco Verratti, mai shekara 24. (Don Balon - via Daily Star)

Watford tana tattaunawa kan dan wasan Chelsea Nathaniel Chalobah kuma tana da karfin gwuiwar cewar mai shekara 22 yana son ya komawaVicarage Road. (London Evening Standard)

Mai tsaron gidan Southampton Paulo Gazzaniga yana dab da barin kulob din a lokacin da kulob-kulob ke nemansa a kan bashi ko kuma kontiragi na din-din-din. (Daily Echo)

Daily Star
The Daily Star back page says Chelsea boss Antonio Conte is "fuming" after striker Romelu Lukaku agreed to join Manchester United from Everton

A wata sabuwa kuma...

Ma'aikatan McDonald biyu sun samu sun dauki hoto da kaftin din Manchester United, Wayne Rooney, a lokacin yake tafiya a hanyar gidan sayar da abincin.(Twitter)

Hakkin mallakar hoto Fred Reardon
Image caption Wayne Rooney da dansa

An tilasta wa Manchester United cire wani sakon da ya nuna Henrikh Mkhitaryan yana tallan rigar 'yan kwallon United inda magoya baya suka ce dan wasan dan asalin Armenia ya yi kaman yana da "ciki". (Mirror)

Hakkin mallakar hoto Twitter

Kociyan Chelsea, Antonio Conte, ya kai ma'aikatansa da iyalansu wani hutu irin na kasaita a Sardinia bayan ya lashe gasar Firimiya. (Sun)

Dan wasan gaban Portugal, Cristiano Ronaldo, ya kaddamar da takalman kwallon kafa guda domin tunawa da lokacin da ya yi yana taka leda a Manchester United da kuma Real Madrid. (Daily Mirror)

Sir Alex Ferguson ya shaida wa abokansa cewar da shi ne kociyan United da ya sayi tsohon dan wasan Chelsea, John Terry .(Sun)

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba