Ebola ya kai zagayen gaba a damben mota

Damben gargajiya
Image caption A ranar Litinin aka fara gasar damben cin mota a birnin Kanon Nigeria

Abdurrazak Ebola ya kai wasan zagaye na uku a gasar damben cin mota da ake yi a birnin Kanon Nigeria.

Ebolan dan wasan Kudu ya yi nasara ne a kan Dogon Danbunza daga Arewa, bayan da Danbunza ya fita daga da'irar filin dambe ba a tashi daga wasa ba, wanda hakan hukuncin kora ce ga dan wasa.

Shi kuwa Shagon Dan Bature daga Arewa ya kai zagayen gaba ne, bayan da Autan Bahagon Sani Mai Maciji daga Kudu bai halarci filin wasan ba.

Alin Saiwa daga Kudu ya samu nasarar doke Abba Shagon Rogget daga Arewa a turmin farko, shi ma Dan Sama'ila daga Kudu a turmin farko ya buge Shagon Shagon 'yan Sanda daga Arewa.

Sani Shagon Kwarkwada daga Kudu kuwa ya kai zagaye na uku ne bayan da aka yi kuri'a tsakaninsa da Dan Ibro Shagon Amadi daga Arewa, bayan da suka tashi canjaras.

Jumulla a dambe biyar da aka yi 'yan wasan Kudu su hudu sun yi nasarar kai wa wasan zagaye na uku, yayin da Arewa ta yi nasara a guda daya.

Labarai masu alaka