Chelsea ta dauki Rudiger daga Roma

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rudiger ya ci kofin zakarun nahiyoyi da aka yi a Rasha

Mai rike da kofin Premier Chelsea ta dauki dan wasan Roma, Antonio Rudiger kan yarjejeniyar shekara biyar, kan kudin fam miliyan 29.

Dan wasan mai tsaron baya ya koma Roma daga VfB Stuttgart wadda ya yi wa wasa 66 ya ci kwallo biyu kacal.

Rudiger ya fara buga wa Roma tamaula a 2015, tuni kuma ya yi mata wasa 56 ya ci kwallo 2.

Dan kwallon mai shekara 24 ya koma Chelsea bayan da ya taimaka wa tawagar kwallon kafa ta Jamus ta lashe kofin Zakarun nahiyoyi da aka kammala a Rasha.

Rudiger zai saka riga mai lamba biyu ta Branislav Ivanovic wanda ya koma Zenit St Petersburg da taka-leda a watan Fabrairu.

Labarai masu alaka