Wikki ta samu maki uku a kan Kano Pillars

Nigerian Premier League Hakkin mallakar hoto LMCNPFL Twitter
Image caption Wikki ta samu maki uku a Kano Pillars a wasan mako na 28 a gasar Firimiyar Nigeria da suka fafata

Kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist ta garin Bauchi ta ci Kano Pillars 2-0 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria wasan mako na 28 da suka fafata a ranar Lahadi.

Wikki ta fara cin kwallo ta hannun Ahmed Usman a minti na 10 da fara tamaula, bayan da aka dawo ne daga hutu ta kata ta biyu ta hannun Chinedu Onyelonu.

Da wannan sakamakon Wikki Tourist ta ci wasanninta takwas da ta buga a jere a gida a kwanan nan.

Ga sakamakon wasu karawar da aka yi a gasar ta Firimiyar Nigeria:

  • Rangers 1-1 3SC
  • Katsina 2-1 Lobi
  • Enyimba 3-0 Tornadoes
  • Plateau Utd 3-0 Akwa Utd
  • Gombe Utd 2-0 El-Kanemi
  • Abia Warriors 2-0 Nasarawa Utd
  • ABS 2-4 Sunshine Stars

Labarai masu alaka