Sevilla ta amince ta sayi Amavi daga Villa

Sevilla Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jordan Amavi ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Faransa ta matasa 'yan kasa da shekara 21 wasa 10.

Aston Villa ta amince ta sayar wa da Sevilla Jordan Amavi, amma ba ta fayyace kudin da za a biya ta ba.

Amavi mai shekara 23, zai koma Sevilla kan yarjejeniyar shekara biyar idan har aka kammala duba lafiyarsa a Spaniya.

Dan wasan ya koma Villa daga Nice a cikin Yunin 2015, ya kuma yi mata wasa 48.

Amavi ya yi fama da jinyar raunin da ya ji a gwiwar kafarsa, sai dai ya koma taka-leda a kakar da aka kammala, inda Villa ta kare a mataki na 13 a Championship.