Wayne Rooney na hakon lashe kofi bayan komawa Everton

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wayne Rooney ya nemi komawa Goodison Park after rejecting a club-record contract offer from Everton before joining Manchester United in 2004

Wayne Rooney ya ce ci wa Everton kofi zai kasance kololuwar nasara a gare shi, bayan ya koma kungiyar daga Manchester United.

A zaman Rooney na shekara 13 a United ya samu kofin gasar Premier biyar da na gasar kalubale uku da na gasar zakarun Turai daya da kuma na gasar Europa daya.

Yana son Everton su ci babban kofin na farko tun kofin kalubale na shekarar 1995 da suka ci.

"Ya kamata wannan kungiyar kwallon kafar ta yi ta cin kofuna, kuma muna daukar muhimman matakai domin mu ci kofuna," in ji Rooney.

Da aka tambaye shi hakan na nufin yana son ya lashe kofi da Everton, sai Rooney ya kara da cewar: "Wannan zai kasance kololuwa saboda na tuna wasan karshe na gasar kalubale a shekarar 1995, ina wurin a matsayi na na dan shekara tara, kuma a ce wannan ne kofi na karshe... Ya kamata a ce Everton ta lashe karin kofuna tun wannan lokacin."

Everton, wadda ta kashe sama da fam miliyan 90 a kasuwar 'yan wasa na lokacin bazara, ta cimma wata yarjejeniyar sayan fili a Liverpool domin gina wani filin wasa na Fam miliyan 300.

Rooney, wanda aka bayyana komarwarsa Goodison Park kan yarjejeniyar shekara biyu ranar Lahadi, ya kara da cewar : "Domin sabon filin wasan da ake shirin ginawa, wannan wani lokaci ne mai dadi mutum ya kasance dan wasan Everton ko magoya bayan Everton.

"Ya wajaba a kan mu 'yan wasa mu sa wannan lokacin ya kara dadi ta hanyar taka leda da kyau kuma mu yi kokarin taimakawa kungiyar ta yi nasara, mu kuma kawo kafuna kulob din.

"Ina da yakinin cewar muna da karfin yin ansara a gasar Firimiya da kuma kofuna a wasu gasannin, lallai za mu iya lashe daya daga cikin wadannan kofunan."

Rooney dan shekara 31 zai saka riga lamba 10 wadda a kakar bara ya kasance ta Romelu Lukaku ce, wanda zai koma Manchester United kan kudi Fam miliyan 75.

Rooney shi ne dan wasa na shida da Everton za ta saya tun da aka kammala kakar 2016-17, inda ta kasance ta bakwai a teburin gasar Firimiya.

Baya ga tsohon keftin din Ingila Rooney, mai tsaron gida Jordan Pickford da dan wasan bayan Ingila Michael Keane, dan wasan tsakiyar Netherlands Davy Klaassen da dan wasan gaba Sandro Ramirez da kuma Henry Onyekuru sun koma Everton da taka leda a lokacin bazarar nan.

Rooney ya ce, "Ina matukar jin cewar kungiyar na tafiya yadda ya kamata, tana shigowa da irin 'yan wasan da suka dace. Ina son in kasance tare da ita, kuma ina fatan in kasance tare da kungiyar Everton mai nasara."

Rooney, wanda ya sha kwallaye 53 a wasanni 119 da ya buga wa Ingila, ba zai dade kafin ya koma Old Trafford ba domin Everton za ta ziyarci United a gasar Firimiya ranar 17 ga watan Saptumba.

Tarihin yadda taka ledan Rooney ke raguwa a gasar Firimiya
Kaka Wasannin da ya buga Yawan mintunan da ya yi a fili Wasannin da aka fara da shi Wasannin da ya buga ba a fara da shi ba
2013-14 29 2,448 27 2
2014-15 33 2,876 33 0
2015-16 28 2,410 27 1
2016-17 25 1,539 15 10

'Wayne ya dawo gida'

Kociyan Everton Ronald Koeman ya yi imani cewar kwarewar Rooney za ta taimaka matuka a kungiyar da ba da wadanda suka lashe kofuna da yawa.

"Babu wanda ya lashe kofuna a cikin 'yan wasan in ban da Gareth Barry [Manchester City] da Davy Klassen [Ajax]," in ji Koeman. "Ka da ka manta yadda kwarewarsa za ta taimaka wa sauran 'yan wasan.

"Har yanzu dai Wayne zai iya taka rawar gani - zai ci gaba da kasancewa zakaran gwajin dafi - kuma yana son ya taka leda a mataki mafi girma da zai iya samu.

"Gidansa ne kuma yana son gogayya, yana son kalubale.

"Abubuwan da suka sa ya fita daban sune yadda yake yi kan kwallo da kwarewarsa da kuma abun da na siffanta da tunaninsa na cin wasa.

"Kowa ya sani cewar zai iya buga ko ina a gaba. Dan wasa ne mai kaifin basira. Kwararren dan wasa ne kuma wannan zai taimaka wa kowa."

'Na shafe shekaru ina saka raigar barcin Everton'

Rooney ya ce shi ya ji dadin sake saka rigar Everton bayan ya shafe shekara 13 United.

Duk da haka, ya bayyana a hirarsa da gidan talabijin na Everton cewar ya dade yana sanya shudin kaya a boye da daddare.

"Na boye batun na tsawon shekara 13, amman na kasance mai saka rigar barcin Everton a gida da yarana," in ji Rooney. "Dole in dan boye wannan!

"Na ji irin dadi na musamman da na da saka rigar shekara 13 da ya wuce, kuma yanzu ina fatan ranar da zan fita filin wasa ne da shi."

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba