Chelsea ta kara bai wa Diego Costa hutu

Costa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Costa ya koma Chelsea daga Atl├ętico Madrid a shekarar 2014

An bai wa dan wasan gaban Chelsea Diego Costa karin hutu, wanda hakan yake nuni da cewa watakila kulob din zai sallame shi a kakar saye da sayar da 'yan wasa.

Ana danganta dan wasan mai shekara 28 da shirin barin kulob din bayan da kocin Chelsea Antonio Conte ya ce baya cikin 'yan wasansa na farko da zai yi amfani da shi.

Costa bai yi atisaye ba a ranar Litinin, watakila hakan ya faru ne don kaucewa ce-ce-ku-ce.

"Kulob din ne da dan wasan da kansa suka amince ya kara hutun kwanakin," in ji wata sanarwa daga shafin Chelsea a Intanet.

Ana saran Costa ba zai halarci atisayen ba har zuwa karshen makon nan.

Costa ne kadai dan wasan da ba zai yi atisayen ba da Chelsea, ban da sabon dan kwallo Antonio Rudiger wanda ya koma Stamford Bridge da taka-leda a ranar Lahadi.

Labarai masu alaka