Man United ta kammala daukar Lukaku

Manchester United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mourinho yana jan ragamar Chelsea ta bayar da Lukaku aro ga Everton

Manchester United ta kammala daukar Romelu Lukaku daga Everton kan kudi fam miliyan 75 kan yarjejeniyar shekara biyar.

Tun farko BBC ta ruwaito cewar Lukaku mai shekara 24 yana da karin fam miliyan 15 kudin tsarabe-tsaren wasa.

Mourinho ne ke jan ragamar Chelsea a lokacin da kungiyar ta sayar da Lukaku ga Everton kan kudi fam miliyan 28 a watan Yulin 2014.

Dan wasan ya buga tamaula aro a Everton a 2013/14 daga baya ta dauke shi kan yarjejeniyar shekara biyar.

Lukaku ya ci kwallo 68 a gasar Premier a kakar wasa biyu da ya buga wa Everton.

Labarai masu alaka