Swansea ta yi wa Sigurdsson farashin £50m

Swansea City Hakkin mallakar hoto Huw Evans picture agency
Image caption Sigursson yana taka rawar gani a Swansea City wadda ta fuskanci kalubalen gasar Premier da ta kare

Kungiyar Swansea City ta yi wa Gylfi Sigurdsson farashin fam miliyan 50, bayan da ta ki sallama tayin fam miliyan 40 da Leicester City ta yi wa dan kwallon.

Sigurdsson mai shekara 27, ya ci wa Swansea kwallo tara ya kuma taimaka aka zura 13 a raga a gasar Premier da aka kammala.

Dan wasan yana da sauran yarjejeniyar shekara uku a Swansea wadda ya saka hannu a kungiyar a matakin dan kwallon da ya fi daukar albashi a kakar da ta wuce.

Sigurdson ya ci kwallo 30 tun komawarsa Swansea a 2014 daga Tottenham.