Real Madrid ta gabatar da Hernandez

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Dan kwallon ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara shida

Theo Hernandez ya taka filin Santiago Bernabeu a karon farko a matsayin dan wasan Real Madrid.

Real ta gabatar da dan kwallon a gaban magoya bayanta a ranar Litinin, sannan ya gana da 'yan jarida.

Madrid ta dauko Hernandez mai tsaron baya mai shekara 19 daga Atletico Madrid, kan yarjejeniyar shekara shida.

Theo ya saka riga mai lamba 15, daga baya ne ya buga wa 'yan kallo kwallon da ke hannunsa.

Labarai masu alaka