Arsene Wenger ya musanta cewar Sanchez zai bar Arsenal

Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption " 'Yan wasan sun kulla yarjejeniya, kuma muna fatan za su mutunta yarjejeniyar" - Arsene Wenger

Alexis Sanchez bai shaida wa Arsene Wenger cewar shi zai bar kulob din ba, in ji kocin Gunners wanda ke fatan dan asalin Chilen zai kammala kontiraginsa.

Dan wasan mai shekara 28 yana da sauran shekara daya a kontiraginsa da Emirates.

Duk da haka, rahotanni sun ambato Sanchez na cewa yana son ya koma kungiyar hamayyar Arsernal a gasar Firimiya, wato Manchester City.

Da aka tambaye shi cewar ko Sanchez ya gaya masa zai kulob din, sai kocin dan asalin Faransa ya ce: "A 'a."

Wenger ya kara da cewar: "'Yan wasan sun kulla yarjejeniya, kuma muna fatan za su mutunta yarjejeniyar. Abun da muke so kenan."

Sanchez ya koma Arsenal ne daga Barcelona a lokacin bazarar shekarar 2014.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal ta buga wasan sada zumunci biyu a wannan makon

'Daukacin Turai na marabtar Mbappe hannu-bibbiyu'

Wenger, wanda ke kasar Australiya da tawagar Arsenal domin atisayen gabannin kakar bana, ya kuma yi bayani game da yadda yake son dan wasan gaban Monaco, Kylian Mbappe.

Dan shekara 18 din ya kasance maudu'in hasashen ciniki bayan ya taka rawar gani a kakar bara in da ya sha kwallaye 29.

"Wani dan wasa ne wanda in ya tashi da safe, zai iya zabi in da yake son ya tafi," in ji Wenger.

"Ba kasafai ake samun'yan wasa masu irin wannan sa'ar ba domin shi dan shekara 18 ne kawai, kuma daukacin Turai na marabtarsa.

"Babu wanda zai ce shi ba ya son irin wannan dan wasan, dukkan kungiyoyin kwallon kafa) na son sa."

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba