Rodriguez zai buga wa Munich wasanni aro

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rodriguez ya koma Madrid da taka-leda a 2014

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta amince ta bai wa Bayern Munich aron James Rodriguez domin ya buga mata tamaula.

Munich din ta amince da Rodriguez ya taka mata leda tsawon shekara biyu da zarar ta gwada lafiyar dan kwallon.

Real ta sanar da labarin ne a shafinta na Intanet, inda ta kara da cewar bayan shekara biyu Munich din tana da zabin sayen dan wasan ko akasin hakan.

Rodriguez ya taka-leda karkashin kociyan Munich, Carlo Ancelotti a lokacin da ya yi aiki a Real Madrid.

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Colombia ya koma Real Madrid a shekarar 2014.

Labarai masu alaka