Madrid ta isa Amurka da 'yan wasa 26

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid za ta yi wasannin atisayen tunkarar kakar bana da za a fara cikin Agusta

Real Madrid ta sauka a Amurka a ranar Talata da 'yan wasa 26 domin fara atisayen tunkarar gasar da za a fara a bana.

Madrid wadda ta sauka a birnin Los Angeles za ta kara da Manchester United da Manchester City da Barcelona a gasar International Champions Cup.

Haka kuma kungiyar za ta kece raini da fitattun 'yan wasan gasar Amurka a wasan sada zumunta.

Real wadda ta ci La Liga da kofin Zakarun Turai a kakar da aka kammala, za ta kara da Manchester United a ranar takwas ga watan Agusta a European Super Cup.

Ga jerin 'yan wasan da Madrid ta je da su Amurka:

Masu tsaron baya: Keylor Navas, Casilla, Rubén Yáñez and Luca.

Masu tsaron baya: Carvajal, Varane, Nacho, Marcelo, Theo, Danilo, Quezada, Tejero, Achraf da kuma Manu Hernando.

Masu wasan tsakiya: Kroos, Casemiro, Modric, Isco, Kovacic, Óscar da kuma Franchu.

Masu cin kwallo: Benzema, Bale, Lucas Vázquez, Morata da kuma Dani Gómez.