Barcelona za ta dawo atisaye ranar Laraba

Barcelona

Asalin hoton, Barcelona FC

Bayanan hoto,

Lokacin da ake duba lafiyar Rikitic a 2016/17

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona za ta dawo atisaye a ranar Laraba a filin Ciutat Esportiva Joan Gamfer domin tunkarar kakar da za a fara a bana.

Tun da sanyin safiya za a fara duba lafiyar 'yan wasa 18, kuma hudu daga cikinsu daga matasan kungiyar suke.

A kuma lokacin ne sabon kociyan Barcelona, Ernesto Valverde zai fara aiki da kungiyar da ya koma a karshen kakar da ta kare, bayan da Luis Enrique ya yi ritaya.

Sai a ranar Juma'a ne Sergio da Denis Suarez da Iniesta da Jordi Alba da Digne da kuma Umtiti za su fara atisayen sakamakon wasannin da suka yi wa kasashensu a watan Yuni.

A ranar Asabar ake sa ran Messi da Neymar da Arda da kuma Pique, yayin da aka bai wa Ter Stegen da Andre Gomes hutu sakamakon gasar Confederation da suka bugawa Jamus.