Ozil zai ci gaba da zama a Arsenal

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A karshen kakar 2018 yarjejeniyar Ozil za ta kare a Emirates

Mesut Ozil ya ce yana son ya ci gaba da taka-leda a Arsenal, kuma zai tattauna da mahukuntan kungiyar kan tsawaita zamansa.

Dan kwallon ya ce da zarar Arsenal ta dawo daga wasannin atisayen da za ta yi a Australia da China za su zauna domin batun tsawaita yarjejeniyarsa a Emirates.

Ozil mai shekara 28, yana da kwantiragi da Arsenal zuwa 2018, amma ana ta rade-radi kan makomarsa a kungiyar.

Arsenal za ta kara da Sydney a ranar Alhamis da kuma Western Sydney Wanderers a ranar Asabar, sannan ta nufi kasar China.

A kasar China Arsenal za ta kece raini da Bayern Munich a ranar 19 da watan Yuli a Shanghai da kuma Chelsea a ranar 22 ga watan a Beijing daga nan ta koma Ingila.

Labarai masu alaka