Dani Alves ya koma Paris St-Germain

PSG Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alves yaq buga wa Barcelona wasa karkashin Pep Guardiola

Dan kwallon tawagar Brazil, Dani Alves ya koma Paris St-Germain da taka-leda, bayan da yarjejeniyarsa da Juventus ta kare a bana.

Alves wanda Manchester City ta dinga zawarci ruwa a jallo ya amince ya buga wa PSG, maimakon ya sake wasa karkashin Pep Guardiola wanda ya horar da shi a Barcelona.

City ta so ta bai wa Alves mai shekara 34 kwantiragin shekara biyu, amma ba za ta iya biyan fam 230,000 da PSG ake cewa za ta dinga biyansa a duk mako ba.

Manchester City yanzu ta koma neman mai tsaron bayan Tottenham Kyle Walker