Carrick ya zama kyaftin din Man United

Manchester United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Carrick ne dan kwallon da ya fi dadewa a Old Trafford

Kungiyar Manchester United ta nada Micheal Carrick a matsayin kyaftin dinta, wanda shi ne dan kwallon da ya fi dadewa a Old Trafford.

Carrick mai shekara 35, ya koma United a shekarar 2006, ya kuma maye gurbin Wayne Rooney wanda ya koma Everton da taka-leda.

Dan kwallon ya koma United daga Tottenham kan kudi fam miliyan 18.6 ya kuma kulla yarjejeniyar ci gaba da zama a Old Trafford zuwa Junin 2018 a shekarar nan.

Carrick ya buga wa United wasa 459, ya kuma lashe kofin Premier biyar da na FA da na Zakarun Turai.

Labarai masu alaka