An ya Gylfi Sigurdsson zai ci gaba da zama a Swansea kuwa?

Gylfi Sigurdsson Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Gylfi Sigurdsson ya zura kwallo tara kuma ya taiamaka aka ci 13 a kakar bara a gasar Firimiya

Gylfi Sigurdsson ba zai bi 'yan tawagar Swansea zuwa Amurka ba a wasannin gabannin kakar da za su yi, lamarin da yake kara rade-radin cewar zai bar kungiyar.

Wannan labarin ya zo ne bayan kociya Paul Clement ya ce ta yi wu kulob din ya sayar da shi.

Swansea suna neman fam miliyan 50 ne kan dan wasan tsakiyar.

Kungiyar ta wallafa a shafinta na Twitter cewar: "Bayan ya buga wasan da muka yi da Barnet jiya da daddare, Gylfi ya fara jin ba zai iya tafiyar ba saboda halin rashin tabbas da ake ciki kan makomarsa."

Swansea ta yi watsi da tayin fam miliyan 40 da Leicester City ta yi kan dan wasan, amman Clement ya ce bisa la'akari da kasuwancin kwallon kafa zai iya zama dole kungiyra ta sayar da shi.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba