Man City na daf da daukar Walker

Manchester City Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Walker zai koma City bayan da ta kasa sayen Dani Alves daga Juventus

Manchester City ta kusa kammala sayen dan wasan Tottenham, Kyle Walker, bayan da ta amince ta biya fam miliyan 50.

A ranar Juma'a ake sa ran Walker mai shekara 27 zai je Ettihad domin a duba lafiyarsa.

Walker ya koma Tottenham da taka-leda daga Sheffield United a 2009, sai dai ba zai buga wa Spurs wasannin atisayen tunkakar gasar bana ba.

Mai makon hakan zai bi Manchester City zuwa Amurka a ranar Litinin, inda za ta fafata a wasanni sada zumunta.

A karshen kakar da ta kare ne City ta sallami masu tsaron bayanta uku ciki har da Pablo Zabaleta da Bacary Sagna.

A ranar Laraba ne Dani Alves ya amince ya koma PSG da taka-leda maimakon Manchester City.

Labarai masu alaka