Madrid ce ta daya a iya kwallo a Turai

Kai tsaye Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid za ta buga wasannin atisaye a Amurka don tunkarar kakar bana

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai ta bayyana Real Madrid a mataki na daya a jadawalin kungiyoyin da suke taka-leda a nahiyar.

Madrid wadda ta lashe kofin La Liga da na Zakarun Turai a kakar da ta kare tana da maki 151.799, kuma matsayin da take kai tun karshen kakar 2013/14.

Atletico Madrid ce ta biyu da maki 133.799 sai Barcelona biye da maki 128.799 sannan Bayern Munich da maki 122.656 da kuma Juventus a mataki na biyar da maki 119.049 a biyar din farko.

Hukumar tana auna kokarin kungiyoyin nahiyar bisa kwazon da suke yi a gasar cin kofin Zakarun Turai da ta Europa tsawon shekara biyar.

Labarai masu alaka