Manchester United ta fi kowanne kulob 'arziki a duniya'

Man Utd Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester United ta mallaki dala biliyan uku da miliyan 690

Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester United ita ce ta fi arziki a sahun kungiyoyin kwallon kafa na duniya, inda ta mallaki dala biliyan 3.69, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana a kididdigarta ta bana.

Dallas Cowboys, wato kungiyar wasan kwallon zarin-ruga ta kasar Amurka ta kare kambunta na zama kungiyar wasannin da ta fi arziki a duniya inda ta mallaki Dala biliyan 4.2, kamar yadda Forbes ta bayyana.

Barcelona ita ce ta zo ta biyu a jerin kwallon kafa inda ta mallaki dala biliyan 3.64, sai Real Madrid a mataki na uku da dala biliyan 3.58.

Ga jerin kungiyoyin wasannin da suka fi arziki a duniya

1. Dallas Cowboys - wasan kwallon zari-ruga $4.2bn

2. New York Yankees - wasan kwallon baseball $3.7bn

3. Manchester United - wasan kwallon kafa, sun mallaki $3.69bn

4. Barcelona - wasan kwallon kafa, sun mallaki $3.64bn

5. Real Madrid - wasan kwallon kafa, sun mallaki $3.58bn

6. New England Patriots - wasan kwallon zari-ruga, sun mallaki $3.4bn

7. New York Knicks - wasan kwallon baseball, sun mallaki $3.3bn

8. New York Giants - wasan kwallon zari-ruga, sun mallaki $3.1bn

9. San Francisco 49ers - wasan kwallon zari-ruga, sun mallaki $3bn

10. Los Angeles Lakers - wasan kwallon baseball, sun mallaki $3bn

Labarai masu alaka