Kyle Walker: Man City ta sayi dan wasan Tottenham kan fam 45m

Kyle Walker Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kyle Walker ya taka wa Ingila leda sau 27

Manchester City ta kammala sayar dan wasan Tottenham da Ingila Kyle Walker kan kudi fam miliyan 45.

Walker, wanda ya buga wa Ingila wasanni 27 kuma ya shafe kaka takwas a Spurs, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da City.

Yarjejeniyar, wadda ta kai fam miliyan 50 har da karin fam miliyan 5, ka iya mayar da shi dan wasan Ingila mafi tsada a tarihi.

Walker ya ce: "Na yi murnar rattaba wa City hannu, kuma ina shaukin na fara musu wasa. Pep Guardiola daya ne daga cikin kociyoyin da aka fi girmamawa a duniya."

Walker, wanda ya koma Spurs daga Sheffield United a shekarar 2009 kuma ya buga wasannin Firimiya 183, ya kara da cewa: "Ina jin zai iya ciyar da wasa na gaba."

Dan shekara 27 din, wanda zai saka riga mai lamba biyu, a na tsammanin zai bi City tafiyar da za su yi zuwa Amurka ranar Litinin.

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba