Barcelona ta sake sayan Gerard Deulofeu daga Everton

Gerard Deulofeu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gerard Deulofeu ya koyi wasan kwallon kafa a makarantar Barcelona, kuma ya koma kulob din yana dan shekara 9

Barcelona ta sake sayan dan wasan gefe Gerard Deulofeu daga Everton bisa wata yarjejeniyar da ake ganin ta kai fam miliyan 10.6.

Da farko Deulofeu ya je Everton ne kan aro a kakar 2013-2014, sannan ya rattaba hannu kan yarjejeniyar din-dindin a shekarar 2015.

Dan wasan mai shekara 23 ya buga wa Everton wasanni 13 a kakar bara kafin ya koma AC Milan a watan Janairu.

Dan Spaniyan, wanda ya ke dan makarantar 'koyon kwallo ta Barcalona da ke Nou Camp ne, ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar shekara biyu.

Bayan ya samu kaka mai kyau a Merseyside, Deulofeu ya bata da kociya Ronald Koeman wanda ya ba shi damar zama a Italiya a kashi na biyu na kakar bara.

Ya buga wasanni 36 da farko, kuma ya buga 39 bayan an fara wasa inda ya sha kwallaye takwas. Da ya cigaba da zama, da kwantiraginsa ya kai watan Yunin shekarar 2018.

Deulofeu ya ce: "Ina matukar farin cikin komawa gida. Ina shaukin in fara wannan aiki. Na dade ina son in kasance a nan."

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba