Akwai yiwuwar Ibrahimovic zai zauna a Man Utd – Mourinho

Ibrahimovic Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ibrahimovic ya koma Manchester United ne a bara daga Paris St-Germain

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce "akwai yiwuwar" a sabunta kwantiragin Zlatan Ibrahimovic wanda ya kare a watan jiya.

Da kulob din ya ki sabunta kwantiragin tsohon dan wasan tawagar kasar Sweden din ne.

Har ila yau, dan wasan mi shekara 35 ya fara murmurewa daga raunin da ya ji a gwiwa.

Mourinho ya ce "Idan aka yanke shawarar cewa Ibrahimovic ya tsaya ya jira har sai watan Disamba - ba zai dawo ba sai lokacin - me zai hana? Muna tattaunawa kuma muna shawarwari."

A watan Yulin shekarar 2016 ne Ibrahimovic ya koma Man U bisa yarjejeniyar shekara daya, amma ba a tsawaita yarjejeniyar bayan da ya ji rauni a watan Afrilun da ya gabata.

Dan wasan ya yi wa United wasa 46 wadanda a ciki ya zura kwallaye 28 a raga.

Mourinho ya ce yana so ya kara sayen 'yan wasa "daya ko biyu" a kakar bana.

Labarai masu alaka